29 Aka sa waɗansu su zama masu lura da kayayyakin Haikalin, da kayayyakin aiki na cikin Wuri Mai Tsarki, da lallausan gari, da ruwan inabi, da mai, da turare, da kayan yaji.
30 Waɗansu 'ya'yan firistoci, maza, suke harhaɗa kayan yaji.
31 Mattitiya, ɗaya daga cikin Lawiyawa, ɗan farin Shallum na iyalin Kora, shi ne mai lura da toya waina.
32 Waɗansu 'yan'uwansu Kohatawa suke lura da gurasar ajiyewa. Sukan shirya ta kowace Asabar.
33 Waɗannan su ne mawaƙa, da shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa, waɗanda suka zauna a ɗakunan Haikali, ba su yin wani aiki dabam, gama dare da rana suke yin aikinsu.
34 Waɗannan su ne manyan shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa a zamaninsu, wato waɗanda suka zauna a Urushalima.
35 Yehiyel ne ya kafa Gibeyon ya zauna a ciki, sunan matarsa Ma'aka,