10 Domin haka takobi ba zai rabu da gidanka ba, domin ka raina ni, ka ɗauki matar Uriya Bahitte ta zama matarka.
11 Na rantse zan sa wani daga cikin iyalinka ya far maka da tashin hankali. A idonka zan ba da matanka ga wani mutum. Zai kwana da su da rana katā.
12 Kai, a ɓoye ka yi naka zunubi, amma zan sa a yi maka a gaban dukan mutanen Isra'ila da rana katā.’ ”
13 Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.”Natan ya ce masa, “Ubangiji ya gafarta maka, ba za ka mutu ba.
14 Amma domin ka ba da ƙofa ga magabtan Ubangiji su zarge shi, wato saboda abin da ka aikata, ɗan da za a haifa maka zai mutu.”
15 Sa'an nan Natan ya tafi gida.Ubangiji kuwa ya sa ciwo ya kama yaron da matar Uriya ta haifa wa Dawuda.
16 Dawuda kuwa ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi. Ya shiga ya kwanta a ƙasa dukan dare.