2 Sam 17 HAU

Hushai Ya Wofintar da Shawarar Ahitofel

1 Ahitofel ya kuma ce wa Absalom, “Bari in zaɓi mutum dubu goma sha biyu (12,000), mu tafi mu bi Dawuda da daren nan.

2 Zan fāɗa masa sa'ad da yake cikin gajiya da karayar zuciya, in firgitar da shi. Dukan mutanen da suke tare da shi za su gudu. Shi kaɗai zan kashe.

3 Zan kawo maka dukan jama'a kamar yadda akan kawo amarya a gidan angonta. Ran mutum guda kaɗai kake nema, sauran mutane duka kuwa su yi zamansu lafiya.”

4 Wannan shawara ta gamshi Absalom da dattawan Isra'ila.

5 Sa'an nan Absalom ya ce, “A kirawo Hushai Ba'arkite don mu ji abin da shi kuma zai faɗa.”

6 Da Hushai ya zo, sai Absalom ya ce masa, “Ga shawarar da Ahitofel ya bayar, mu bi ta? Ko kuwa? Kai, me ka ce?”

7 Sai Hushai ya ce wa Absalom, “A wannan lokaci dai shawarar da Ahitofel ya bayar ba ta da kyau.”

8 Hushai ya ci gaba da cewa, “Ka san tsohonka da jama'arsa jarumawa ne, yanzu a husace suke kamar damisar da aka kwashe wa 'ya'ya a jeji. Tsohonka kuma ya ƙware da sha'anin yaƙi, ba tare da mutanensa zai kwana ba.

9 Yanzu haka yana cikin rami ko dai a wani wuri a ɓoye. Idan an kashe waɗansu daga cikin mutanenka a karo na farko, duk wanda ya ji zai ce, ‘An kashe mutane da yawa daga cikin mutanen Absalom.’

10 Wannan zai sa jarumi wanda yake da zuciya kamar ta zaki ya karaya don tsoro, gama dukan mutanen Isra'ila sun sani tsohonka jarumi ne, su kuma waɗanda suke tare da shi jarumawa ne.

11 Shawarata ita ce a tattara maka dukan Isra'ilawa tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba, yawansu kamar yashi a bakin teku. Kai kuma da kanka ka tafi wurin yaƙin.

12 Da haka za mu tafi mu neme shi duk inda yake, mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo bisa ƙasa. Da shi da mutanensa, ba wanda za a bari da rai.

13 Idan ya gudu zuwa cikin gari, sai dukan jama'armu su zarge garin da igiya, su jā har duk ya watse, yadda ba za a bar wani dutse a kan wani ba.”

14 Sai Absalom da dukan mutanen Isra'ila suka ce, “Shawarar Hushai Ba'arkite ta fi ta Ahitofel kyau.” Haka Ubangiji ya nufa ya wofintar da kyakkyawar shawarar Ahitofel don ya jawo wa Absalom masifa.

An Yi wa Dawuda Sanarwa ya Tsere

15 Sa'an nan Hushai ya ce wa Zadok da Abiyata, firistoci, “Ga irin shawarar da Ahitofel ya ba Absalom da dattawan Isra'ila, ga kuma irin wadda ni na bayar.

16 Yanzu sai ka aika da sauri a faɗa wa Dawuda, kada ya kwana a bakin jeji a daren yau, amma ya haye don kada a hallaka shi tare da mutanensa.”

17 Jonatan da Ahimawaz suna jira a En-rogel. Wata baranya takan tafi ta faɗa musu saƙo, su kuma sai su tafi su faɗa wa sarki Dawuda, don kada a gan su suna shiga birnin.

18 Amma wani saurayi ya gan su, sai ya faɗa wa Absalom. Sai su biyu ɗin suka gudu nan da nan. Suka shiga gidan wani mutum a Bahurim, akwai rijiya a filin gidan. Sai suka shiga rijiyar.

19 Matar gidan kuwa ta yi shimfiɗa a bakin rijiyar, ta baza tsaba a kai, ba kuwa wanda ya san abin da ta yi.

20 Sa'ad da fādawan Absalom suka zo gidan, suka tambayi matar, “Ina Ahimawaz da Jonatan suke?”Sai ta ce musu, “Ai, tuni sun haye kogi.”Sa'ad da suka neme su ba su same su ba, sai suka koma Urushalima.

21 Bayan da fādawan sun tafi, sai mutanen suka fito daga rijiyar. Suka tafi suka ce wa sarki Dawuda, “Ka tashi ka haye kogin nan da nan, gama ka ji irin muguwar shawarar da Ahitofel ya bayar a kanka.”

22 Sai Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka haye Urdun. Kafin wayewar gari ko wannensu ya haye Urdun.

23 Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya yi wa jakinsa shimfiɗa ya hau, ya koma garinsu. Da ya kintsa gidansa, sai ya rataye kansa, ya mutu, aka binne shi a kabarin mahaifinsa.

Dawuda a Mahanayim

24 Dawuda kuwa ya zo Mahanayim. Absalom kuma da dukan mutanen Isra'ila suka haye Urdun.

25 Absalom ya naɗa Amasa ya zama shugaban sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan Yeter ne, Ba'isma'ile, wanda ya auri Abigail 'yar Nahash, 'yar'uwar Zeruya mahaifiyar Yowab.

26 Absalom da mutanen Isra'ila suka kafa sansaninsu a ƙasar Gileyad.

27 Sa'ad da Dawuda ya kai Mahanayim, sai Shobi ɗan Nahash daga Rabba ta Ammonawa, da Makir ɗan Ammiyel daga Lodebar, da Barzillai Bagileyade daga Rogelim,

28 suka kawo wa Dawuda da jama'arsa waɗannan kaya da abinci, wato gadaje, da tasoshi, da tukwane, da alkama, da sha'ir, da gari, da soyayyen hatsi, da wake, da waken barewa,

29 da zuma, da kindirmo, da tumaki, da cukun madarar shanu. Gama sun sani Dawuda da mutanensa suna jin yunwa, da gajiya, da kishi, a cikin jeji.

Surori

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24