4 Sai sarki ya ce musu, “Duk abin da kuka ga ya fi muku kyau, shi zan yi.” Sarki kuwa ya tsaya a bakin ƙofar garin sa'ad da sojojin suke fita, kashi kashi, ɗari ɗari, da dubu dubu.
5 Ya kuma umarci Yowab, da Abishai, da Ittayi ya ce, “Ku lurar mini da saurayin nan, Absalom.” Dukan sojojin suka ji umarnin da sarki ya yi wa shugabanninsu a kan Absalom.
6 Sojojin suka tafi zuwa karkara don su yi yaƙi da mutanen Isra'ila. Suka yi yaƙin a kurmin Ifraimu.
7 Mutanen Isra'ila suka sha kashi a hannun jarumawan Dawuda. A wannan rana aka kashe mutane da yawa, har mutum dubu ashirin (20,000).
8 Yaƙin ya bazu ko'ina a ƙasar. A ranar abin da kurmin ya ci ya fi abin da aka kashe da takobi.
9 Absalom yana cikin gudu sai ya fāɗa a hannun jarumawan Dawuda. Sa'ad da yake cikin gudu a kan alfadarinsa, sai alfadarin ya kurɗa tsakanin rassan babban itacen oak. Kansa ya sarƙafe kam cikin rassan itacen oak ɗin, alfadarin kuwa ya wuce, ya bar shi yana rataye yana lilo.
10 Da wani mutum ya gani, sai ya tafi ya faɗa wa Yowab, ya ce, “Na ga Absalom yana reto a itacen oak.”