21 Abishai ɗan Zeruya kuwa ya ce, “Ya kamata a kashe Shimai gama ya zagi wanda Ubangiji ya zaɓa ya zama sarki.”
22 Amma Dawuda ya ce wa Abishai da ɗan'uwansa Yowab, “Ina ruwana da ku, ku 'ya'yan Zeruya? Kuna so ku jawo mini wahala? Ni ne Sarkin Isra'ila yanzu, don haka ba Ba'isra'ilen da za a kashe a yau.”
23 Sa'an nan ya ce wa Shimai, “Ina tabbatar maka, cewa, ba za a kashe ka ba.”
24 Sa'an nan Mefiboshet jikan Saul ya gangara ya taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har zuwa ranar da ya komo da nasara Mefiboshet bai wanke ƙafafunsa ba, bai kuma yi gyaran fuska ba, bai ma wanke tufafinsa ba.
25 Sa'ad da ya iso daga Urushalima don ya taryi sarki, sai sarki ya ce masa, “Me ya sa ba ka tafi tare da ni ba, Mefiboshet?”
26 Mefiboshet ya amsa ya ce, “Ya ubangijina, sarki, barana ya ruɗe ni, gama na ce masa ya yi wa jaki shimfiɗa don in hau in tafi wurin sarki, gama ka sani ni gurgu ne, ranka ya daɗe.
27 Barana ya ɓata sunana a gaban ubangijina, sarki. Amma ranka ya daɗe, ya sarki, kai kamar mala'ikan Allah kake, sai ka yi abin da ya yi maka daidai.