18 Ya kuɓutar da ni daga waɗanda suke ƙina,Daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina!
19 Sa'ad da nake cikin wahala sun auka mini,Amma Ubangiji ya kiyaye ni.
20 Ya taimake ni ya fisshe ni daga hatsari,Ya cece ni domin yana jin daɗina.
21 “Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina,Ya sa mini albarka domin ba ni da laifin kome.
22 Gama na kiyaye dokar Ubangiji,Ban yi wa Allahna tayarwa ba.
23 Na kiyaye dukan dokokinsa,Ban yi rashin biyayya ga umarnansa ba.
24 Ya sani ni marar laifi ne,Na kiyaye kaina daga aikata mugunta.