1 Gidan Saul da gidan Dawuda suka daɗe suna yaƙi da juna. Ƙarfin gidan Dawuda ya yi ta ƙaruwa, amma na gidan Saul ya yi ta raguwa.
2 'Ya'ya maza da aka haifa wa Dawuda a Hebron ke nan, Ahinowam Bayezreyeliya ta haifa masa ɗan farinsa, Amnon.
3 Abigail, matar marigayi, Nabal Bakarmele, ta haifa masa ɗansa na biyu, Kileyab. Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur, ta haifa masa ɗansa na uku, Absalom.
4 Haggit ta haifa masa ɗansa na huɗu, Adonaija. Abital ta haifa masa ɗansa na biyar, Shefatiya.
5 Matarsa Egla ta haifa masa ɗansa na shida, Itireyam. Dukan waɗannan a Hebron ne aka haife su.