1 Dawuda ya yi tambaya, ko akwai wani da ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna wa alheri saboda Jonatan.
2 Akwai wani bara na gidan Saul, sunansa Ziba. Sai aka kirawo shi wurin sarki Dawuda. Sarki ya tambaye shi, “Kai ne Ziba?”Sai ya amsa, “Ranka ya daɗe, ni ne.”
3 Sa'an nan sarki ya tambaye shi ko akwai wani wanda ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna masa alherin Allah.Ziba ya ce wa sarki, “Akwai ɗan Jonatan, gurgu ne kuwa.”
4 Sai sarki ya tambaye shi, “Ina yake?”Ziba ya ce, “Yana gidan Makir, ɗan Ammiyel a Lodebar.”
5 Sarki kuwa ya aika aka zo da shi daga gidan Makir, ɗan Ammiyel, daga Lodebar.