15 Sa'an nan mala'ikan Ubangiji ya ce wa Iliya, “Ka sauka, ka tafi tare da shi, kada ka ji tsoronsa.” Iliya kuwa ya tashi, ya tafi tare da shi har gaban sarki.
16 Ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, ‘Domin ka aiki manzanni su yi tambaya wurin Ba'alzabul, gunkin Ekron, ba Allah a Isra'ila ne wanda za ka yi tambaya a wurinsa? Domin haka ba za ka sauko daga kan gadon da kake kwance ba, amma za ka mutu lalle.’ ”
17 Ahaziya kuwa ya mutu bisa ga maganar Ubangiji, daidai yadda Iliya ya faɗa. Sai ɗan'uwansa Yehoram ya gāji gadon sarautarsa a shekara ta biyu ta Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, gama Ahaziya ba shi da ɗa.
18 Sauran ayyukan da Ahaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.