16 Ya ce, “Ka zo tare da ni, ka ga kishin da nake da shi domin Ubangiji.” Sai suka tafi cikin karusarsa.
17 Da suka isa Samariya, sai ya kashe duk wanda ya ragu na gidan Ahab a Samariya. Ya share mutanen gidan Ahab kaf kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi Iliya.
18 Yehu kuwa ya tara mutane duka, ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba'al kaɗan, amma Yehu zai bauta masa da yawa.
19 Saboda haka, yanzu sai ku kirawo mini dukan annabawan Ba'al, da dukan masu yi masa sujada, da dukan firistocinsa. Kada a manta da wani, gama ina da babbar hadayar da zan miƙa wa Ba'al. Duk wanda bai zo ba, za a kashe shi.” Amma dabara ce Yehu yake yi don ya hallaka waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.
20 Yehu kuma ya sa a yi muhimmin taro saboda Ba'al. Aka kuwa kira taron,
21 sai ya aika cikin Isra'ila duka, dukan masu yi wa Ba'al sujada kuwa suka zo, ba wanda bai zo ba. Suka shiga, suka cika haikalin Ba'al makil daga wannan gefe zuwa wancan.
22 Sa'an nan Yehu ya ce wa wanda yake lura da ɗakin tufafi, “Ku fito da tufafi na dukan waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.” Shi kuwa ya fito musu da tufafin.