26 Suka fitar da gumakan da suke cikin haikalin Ba'al, suka ƙone su.
27 Suka yi kaca kaca da gunkin Ba'al da haikalinsa, suka mai da haikalin ya zama salga har wa yau.
28 Yehu ya kawar da Ba'al daga cikin Isra'ila.
29 Amma bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi. Siffofin maruƙa biyu suna nan a Betel da Dan.
30 Ubangiji kuwa ya ce wa Yehu, “Da yake ka yi abin da yake daidai a gare ni, ka yi wa gidan ahab bisa ga dukan abin da yake a zuciyata, 'ya'yanka, har tsara ta huɗu, za su ci sarautar Isra'ila.”
31 Amma Yehu bai mai da hankali ya yi tafiya a tafarkin Ubangiji Allah na Isra'ila da zuciya ɗaya ba. Bai rabu da zunuban Yerobowam ba, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi.
32 A kwanakin an Ubangiji ya soma rage ƙasar Isra'ila. Hazayel kuwa ya yaƙe su a karkarar Isra'ila,