18 Sai Yowash Sarkin Yahuza ya kwashe dukan kyautai na yardar rai waɗanda Yehoshafat, da Yoram, da Ahaziya, kakanninsa, sarakunan Yahuza suka keɓe, ya kuma kwashe kyauta ta yardar rai ta kansa, da dukan zinariya da aka samu a baitulmalin Haikalin Ubangiji da baitulmalin gidan sarki, ya aika wa Hazayel, Sarkin Suriya. Sa'an nan Hazayel ya tashi ya bar Urushalima.
19 Sauran ayyukan Yowash da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
20 Fādawansa suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidan da yake Millo, a kan hanyar da ta nufi Silla.
21 Yozakar ɗan Shimeyat, da Yehozabad ɗan Shemer su ne fādawansa da suka kashe shi. Aka binne shi a makabartar kakanninsa cikin birnin Dawuda. Amaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.