11 Amma Amaziya bai ji ba. Sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi, ya shiga yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza a Bet-shemesh ta Yahuza.
12 Mutanen Isra'ila suka ci na Yahuza. Sai kowane mutum ya gudu gida.
13 Yehowash Sarkin Isra'ila kuwa ya kama Amaziya, Sarkin Yahuza, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-shemesh. Ya kuma zo Urushalima ya rushe garun Urushalima kamu ɗari huɗu daga Ƙofar Ifraimu zuwa Ƙofar Kusurwa.
14 Ya kwashe dukan zinariya, da azurfa, da dukan kwanonin da suke cikin Haikalin Ubangiji, da na baitulmalin gidan sarki, da mutanen da aka ba da su jingina, sa'an nan ya koma Samariya.
15 Sauran ayyukan Yehowash da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yadda ya yi yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
16 Yehowash ya mutu, aka binne shi a Samariya a makabartar sarakunan Isra'ila, Ɗansa Yerobowam na biyu ya gāji sarautarsa.
17 Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, ya yi shekara goma sha biyar bayan rasuwar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila.