16 Yehowash ya mutu, aka binne shi a Samariya a makabartar sarakunan Isra'ila, Ɗansa Yerobowam na biyu ya gāji sarautarsa.
17 Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, ya yi shekara goma sha biyar bayan rasuwar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila.
18 Sauran ayyukan da Amaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
19 Aka ƙulla makirci a kansa a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma aka aika zuwa Lakish, aka kashe shi a can.
20 Aka kawo gawar a kan dawakai, aka binne a Urushalima a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda.
21 Sai dukan mutanen Yahuza suka ɗauki Azariya mai shekara goma sha shida, suka sarautar da shi don ya gāji tsohonsa Amaziya.
22 Shi ne ya gina Elat, ya mai da ita ta Yahuza bayan rasuwar tsohonsa.