18 Sauran ayyukan da Amaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
19 Aka ƙulla makirci a kansa a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma aka aika zuwa Lakish, aka kashe shi a can.
20 Aka kawo gawar a kan dawakai, aka binne a Urushalima a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda.
21 Sai dukan mutanen Yahuza suka ɗauki Azariya mai shekara goma sha shida, suka sarautar da shi don ya gāji tsohonsa Amaziya.
22 Shi ne ya gina Elat, ya mai da ita ta Yahuza bayan rasuwar tsohonsa.
23 A shekara goma sha biyar ta sarautar Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash Sarkin Isra'ila, ya ci sarauta a Samariya. Ya yi mulki shekara arba'in da ɗaya.
24 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.