19 Tiglatfilesar, mai mulkin Assuriya, ya kawo wa ƙasar yaƙi, Menahem kuwa ya ba Tiglat-filesar talanti dubu (1,000) na azurfa, don dai ya taimake shi yadda sarautarsa za ta kahu sosai.
20 Menahem ya karɓi kuɗin daga mutanen Isra'ila, wato daga attajirai. Ya tilasta wa kowannensu ya ba da azurfa hamsin. Saboda haka Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya ya koma ƙasarsa.
21 Sauran ayyukan Menahem, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
22 Menahem ya mutu, ɗansa Fekahiya ya gaji sarautarsa.
23 A shekara ta hamsin ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Fekahiya ɗan Menahem, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara biyu.
24 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.
25 Sai shugaban sojojinsa, wato Feka, ɗan Remaliya daga Gileyad, tare da mutum hamsin suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe Fekahiya tare da Argob da Ariye a Samariya a fādarsa. Da suka kashe shi, sai Feka ya zama sarki.