1 A shekara ta goma sha biyu ta sarautar Ahaz Samariya Yahuza, Hosheya ɗan Ila ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara tara.
2 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar sauran sarakunan Isra'ila da suka riga shi ba.
3 Sai Shalmanesar Sarkin Assuriya, ya kawo masa yaƙi, Hosheya kuwa ya zama talakansa, yana kai masa haraji.
4 Amma Sarkin Assuriya ya gane Hosheya ya tayar masa, gama ya aiki manzanni wurin So, wato Sarkin Masar, ya kuma ƙi ya kai wa Sarkin Assuriya haraji kamar yadda ya saba yi kowace shekara, Saboda haka sai Sarkin Assuriya ya kama shi ya sa shi a kurkuku.