1 Sa'ad da Ubangiji zai ɗauki Iliya zuwa Sama cikin guguwa, Iliya da Elisha suka kama hanya daga Gilgal.
2 Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni har zuwa Betel.”Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi Betel.
3 Akwai wata ƙungiyar annabawa da take a Betel suka zo, suka ce wa Elisha, “Ko ka sani, yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?”Elisha ya ce, “I, na sani, amma mu bar zancen tukuna.”
4 Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Elisha, ina roƙonka ka dakata a nan gama Ubangiji ya aike ni Yariko.”Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Sai suka tafi Yariko.
5 Ƙungiyar annabawa da take Yariko suka zo wurin Elisha suka ce masa, “Ko ka sani yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?”Ya ce, “Na sani, amma mu bar zancen tukuna.”
6 Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni zuwa Kogin Urdun.”Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi tare.
7 Waɗansu annabawa hamsin kuma suka tafi tare da su. Iliya da Elisha suka tsaya kusa da kogi, annabawa hamsin ɗin suka tsaya da ɗan nisa.