1 Manassa yana da shekara goma sha biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara hamsin da biyar yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Hefziba.
2 Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji, gama ya aikata abubuwa masu banƙyama waɗanda al'umman da Ubangiji ya kora a gaban jama'ar Isra'ila suka aikata.
3 Gama ya gina matsafai a kan tuddai waɗanda Hezekiya tsohonsa ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba'al bagadai, ya kuma yi gunkiyan nan, wato Ashtoret, kamar yadda Ahab, Sarkin Isra'ila, ya yi. Ya yi wa taurari sujada, ya bauta musu.
4 Ya gina bagadai a Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima zan sa sunana.”