4 saboda kuma marasa laifi waɗanda ya kashe, gama ya cika Urushalima da jinin marasa laifi, Ubangiji kuwa ba zai gafarta wa Manassa ba.
5 Sauran ayyukan Yehoyakim da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
6 Yehoyakim ya rasu. Ɗansa Yekoniya ya gāji gadon sarautarsa.
7 Sarkin Masar kuma bai sāke fitowa daga Masar ba, gama Sarkin Babila ya ƙwace dukan ƙasar da take ta Sarkin Masar, tun daga rafin Masar har zuwa Kogin Yufiretis.
8 Yekoniya yana da shekara goma sha takwas sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Nehushta 'yar Elnatan, mutumin Urushalima.
9 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa ya yi.
10 A zamaninsa ne sojojin Nebukadnezzar Sarkin Babila suka zo Urushalima, suka kewaye ta da yaƙi.