1 A shekara ta goma sha takwas ta sarautar Yehoshafat Sarkin Yahuza, Yehoram ɗan Ahab ya zama Sarkin Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha biyu.
2 Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji, amma bai kai na tsohonsa da tsohuwarsa ba, gama ya kawar da ginshiƙin gunkin nan Ba'al wanda tsohonsa ya yi.
3 Duk da haka, bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.
4 Mesha Sarkin Mowab kuwa makiyayin tumaki ni. Yakan ba Sarkin Isra'ila 'yan tumaki dubu ɗari (100,000), da raguna dubu ɗari (100,000) duk da ulunsu, gandu a shekara.
5 Amma da Ahab ya rasu, Sarkin Mowab kuwa ya tayar wa Sarkin Isra'ila.
6 Sai sarki Yehoram ya fita daga Samariya a lokacin, ya tattara Isra'ila duka.