9 Sai ta ce wa mijinta, “Na gane wannan mutum adali ne, mutumin Allah, wanda kullum yakan wuce ta hanyan nan.
10 Bari mu gina masa ɗan ɗaki a kan bene, mu sa masa gado, da tebur, da kujera, da fitila, don duk sa'ad da ya zo ya sauka a wurin.”
11 Wata rana da Elisha ya zo, ya shiga ɗakin, ya huta.
12 Sai ya ce wa baransa, Gehazi, “Kirawo matan nan.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a gabansa.
13 Ya ce wa Gehazi, “Ka tambaye ta me take so in yi mata saboda dukan wannan wahala da ta yi dominmu? Tana so in yi mata magana da sarki ko da shugaban sojoji?”Sai ta ce, “Ai, ina da dukan abin da nake bukata a cikin jama'ata.”
14 Elisha ya ce, “To, me za a yi mata?”Sai Gehazi ya amsa ya ce, “Ai, ba ta da ɗa, mijinta kuwa tsoho ne.”
15 Sai ya ce, “Kirawo ta.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a ƙofar ɗakin.