1 Na'aman kuwa, shugaban sojojin Sarkin Suriya, shi babba ne mai farin jini ƙwarai a wurin ubangidansa, domin ta wurinsa ne Ubangiji ya ba Suriyawa nasara. Shi mutum ne ƙaƙƙarfan jarumi, amma kuma kuturu ne.
2 Daga cikin hare-haren da Suriyawa suke kaiwa, sai suka kama wata yarinya daga ƙasar Isra'ila, aka sa ta zama mai yi wa matar Na'aman aiki.
3 Wata rana sai ta ce wa uwargijyarta, “Da a ce ubangijina yana tare da annabin nan wanda yake Samariya, da ya warkar da shi daga kuturtarsa!”
4 Na'aman kuwa ya tafi, ya faɗa wa ubangidansa, ya ce, “Ka ji abin da yarinyan nan ta ƙasar Isra'ila ta ce?”
5 Sai Sarkin Suriya ya ce, “Ka tafi yanzu, zan aika wa Sarkin Isra'ila da takarda.”Na'aman kuwa ya ɗauki azurfa na talanti goma, zinariya kuma na shekel dubu shida (6,000), da rigunan ado guda goma, ya kama hanya.
6 Ya kai wa Sarkin Isra'ila tarkardar, wadda ta ce, “Sa'ad da wannan takarda ta sadu da kai, ka sani fa, ni ne na aiko barana, Na'aman, wurinka domin ka warkar da shi daga kuturtarsa.”