23 Na'aman kuwa ya ce, “In ka yarda ka karɓi talanti biyu na azurfa.” Ya ƙirga su ya ɗaure kashi biyu, da kuma rigunan ado masu kyau ya ɗora wa barorinsa biyu, ya umarce su su kai wa Gehazi har gida.
24 Sa'ad da Gehazi ya kai tudu, sai ya karɓi kayan daga hannunsu, ya ajiye a gida, sa'an nan ya sallame su, suka tafi.
25 Sai ya shiga, ya tsaya a gaban Elisha, Elisha kuwa ya tambaye shi, “Ina ka tafi, Gehazi?”Sai ya ce, “Ranka ya daɗe ban tafi ko'ina ba.”
26 Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba, sa'ad da mutumin ya juyo daga karusarsa don ya tarye ka? Wannan shi ne lokacin karɓar kuɗi, da riguna, da gonaki na zaitun, da na inabi, da tumaki, da shanu, da barori mata da maza?
27 Saboda haka kuturtar Na'aman za ta kama ka, kai da zuriyarka har abada.”Haka kuwa ya fita a wurinsa kuturu, fari fat kamar auduga.