1 Sulemanu ɗan Dawuda ya kahu sosai cikin mulkinsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi, Ubangiji kuwa ya sa shi ya zama mashahuri.
2 Sulemanu ya yi magana da dukan manya, wato shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da alƙalai, da dukan shugabanni na Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanni.
3 Sa'an nan Sulemanu da dukan waɗanda suke tare da shi, suka tafi masujadar da take a Gibeyon, gama alfarwar sujada ta Allah, wadda Musa, bawan Ubangiji ya yi a jeji, tana can.
4 Amma dai Dawuda ya riga ya ɗauko akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim, ya kawo shi a wurin da ya shirya, gama ya kafa masa alfarwa a Urushalima.
5 Amma bagaden tagulla wanda Bezalel ɗan Uri daga dangin Hur, ya yi, yana a gaban Wuri Mai Tsarki na Ubangiji, sai Sulemanu da taron jama'a suka yi sujada ga Ubangiji a can.
6 Sulemanu kuwa ya haura, ya tafi wurin da bagaden tagulla yake a gaban Ubangiji, a cikin alfarwa ta sujada, ya miƙa hadayun ƙonawa dubu a kansa.