4 Amma dai Dawuda ya riga ya ɗauko akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim, ya kawo shi a wurin da ya shirya, gama ya kafa masa alfarwa a Urushalima.
5 Amma bagaden tagulla wanda Bezalel ɗan Uri daga dangin Hur, ya yi, yana a gaban Wuri Mai Tsarki na Ubangiji, sai Sulemanu da taron jama'a suka yi sujada ga Ubangiji a can.
6 Sulemanu kuwa ya haura, ya tafi wurin da bagaden tagulla yake a gaban Ubangiji, a cikin alfarwa ta sujada, ya miƙa hadayun ƙonawa dubu a kansa.
7 A wannan dare Allah ya bayyana ga Sulemanu, ya ce masa, “Ka roƙe ni abin da kake so in ba ka.”
8 Sai Sulemanu ya ce wa Allah, “Ka nuna wa tsohona Dawuda madawwamiyar ƙaunarka, har ka naɗa ni sarki a matsayinsa.
9 Yanzu fa ya Ubangiji Allah, alkawarin da ka yi wa tsohona ya cika, gama ka naɗa ni sarki a kan jama'a mai yawa kamar turɓaya.
10 Yanzu sai ka ba ni hikima da sani yadda zan iya kai da kawowa a gaban wannan jama'a, gama wa zai iya mulkin wannan jama'a taka mai yawa haka?”