20 Banda Mahalat kuma, sai ya auri Ma'aka 'yar Absalom, wadda ta haifa masa Abaija, da Attai, da Ziza, da kuma Shelomit.
21 Rehobowam ya fi ƙaunar Ma'aka, 'yar Absalom, fiye da dukan matansa, da ƙwaraƙwaransa. Yana kuwa da matan aure goma sha takwas, da ƙwaraƙwarai sittin. 'Ya'yan da ya haifa maza ashirin da takwas ne, 'ya'ya mata kuwa sittin.
22 Sai Rehobowam ya zaɓi Abaija ɗan Ma'aka, ya zama shugaban 'yan'uwansa, gama nufinsa ya zama sarki.
23 Sai ya yi hikima ya rarraba waɗansu 'ya'yansa maza ko'ina cikin gundumomin ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, a dukan birane masu kagara, ya tanada musu abinci a yalwace. Ya kuma samo musu mata masu yawan gaske.