11 A duk lokacin da sarki ya shiga Haikalin Ubangiji, sai matsara su kawo su, daga baya kuma su maishe su a ɗakin matsaran.
12 Da sarki Rehobowam ya ƙasƙantar da kansa, sai fushin Ubangiji ya huce, don haka bai sa aka hallaka shi ƙaƙaf ba, har ma halin zama a ƙasar Yahuza ya yi kyau.
13 Sarki Rehobowam kuwa ya kafa mulkinsa sosai a Urushalima, yana da shekara arba'in da ɗaya da haihuwa ya ci sarauta, ya yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra'ila domin ya sa sunansa a wurin. Sunan tsohuwar Rehobowam Na'ama, Ba'ammoniya.
14 Amma ya aikata mugunta domin bai nemi Ubangiji a zuciyarsa ba.
15 Ayyukan Rehobowam, daga farko har zuwa ƙarshe an rubuta su a littafin tarihin annabi Shemaiya, da na Iddo maigani. Kullum yaƙi ne tsakanin Rehobowam da Yerobowam.
16 Rehobowam fa ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda. Abaija ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.