7 A lokacin nan sai Hanani, maigani, ya zo wurin Asa, Sarkin Yahuza, ya ce masa, “Da yake ka dogara ga Sarkin Suriya, maimakon ka dogara ga Ubangiji Allahnka, shi ya sa rundunar sojojin Sarkin Suriya ta kuɓuta daga hannunka.
8 Ai, Habashawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da karusai da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, sai ya bashe su a hannunka.
9 Idon Ubangiji fa, yana kai da komowa ko'ina a duniya don ya nuna ikonsa ga dukan waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya. Ka yi wauta a cikin wannan al'amari. Tun daga yanzu har zuwa nan gaba za ka yi ta fama da yaƙoƙi.”
10 Sai Asa ya yi fushi da maiganin, ya sa shi a kurkuku saboda maganar da ya yi masa, gama ya husata da shi ƙwarai. A wannan lokaci kuma sai Asa ya ƙuntata wa waɗansu daga cikin jama'a.
11 Ayyukan Asa, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila.
12 A shekara ta talatin da tara ta mulkin Asa, sai wani ciwo ya kama shi a ƙafa. Ciwon kuwa ya tsananta ƙwarai, duk da haka Asa bai nemi taimakon Ubangiji ba, sai na magori.
13 Asa fa ya rasu bayan shekara biyu da ciwon, a shekara ta arba'in da ɗaya ta mulkinsa.