15 To, yanzu, sai ka aiko wa barorinka da alkama, da sha'ir, da mai, da ruwan inabi kamar yadda ka alkawarta.
16 Mu kuwa za mu yanko maka dukan katakan da kake bukata a Lebanon, mu kawo maka su a kan gadajen fito ta hanyar teku, zuwa Yafa, domin ka kwashe ka kai Urushalima.”
17 Sarki Sulemanu ya ƙidaya dukan baƙin da suke a ƙasar Isra'ila, kamar yadda tsohonsa Dawuda ya yi. Yawan baƙin da aka samu sun kai dubu ɗari da dubu hamsin da uku, da ɗari shida (153,600).
18 Sai ya zaɓi mutum dubu saba'in (70,000) daga cikinsu su zama masu ɗaukar kaya, dubu tamanin (80,000) kuma don su riƙa haƙo duwatsu daga tsaunuka, dubu uku da ɗari shida (3,600) kuwa don su zama shugabanni.