1 Yehoshafat ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda tare da kakanninsa, ɗansa kuma ya gāji gadon sarautarsa.
2 Yoram yana da 'yan'uwa maza, su ne Azariya, da Yehiyel, da Zakariya, da Azariya, da Maikel da kuma Shefatiya. Waɗannan 'ya'ya maza ne na Yehoshafat, Sarkin Yahuza.
3 Tsohonsu ya ba su kyautai da yawa na azurfa da zinariya, da abubuwa masu daraja, da birane masu garu a Yahuza, amma ya ba da mulkin ga Yoram, saboda shi ne ɗan fari.
4 Sa'ad da Yoram ya hau gadon sarautar tsohonsa, ya kahu sosai, sai ya karkashe dukan 'yan'uwansa da takobi, ya kuma karkashe waɗansu daga cikin sarakunan Yahuza.
5 Yoram yana da shekara talatin da biyu sa'ad da ya hau gadon sarauta, ya kuwa yi mulki a Urushalima shekara takwas.