1 Sai mazaunan Urushalima suka naɗa Ahaziya, autansa, ya gāji gadon sarauta, saboda ƙungiyar mutanen da suka zo tare da Larabawa a sansanin sun karkashe dukan 'yan'uwansa maza. Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya fara mulki.
2 Ahaziya yana da shekara arba'in da biyu sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara guda a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ataliya jikar Omri.
3 Ya kuma bi gurbin gidan Ahab, gama tsohuwarsa ita ce mai ba shi shawarar yadda zai aikata mugunta.
4 Ya kuwa aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar gidan Ahab, gama su ne mashawartansa bayan rasuwar tsohonsa, wato shawarar da ta kai shi ga lalacewa.
5 Ya kuwa bi shawararsu. Ya tafi tare da Yehoram ɗan Ahab, Sarkin Isra'ila, don su yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya, a Ramot-gileyad. Suriyawa kuwa suka yi wa Yehoram rauni.