1 Amaziya yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara ashirin da tara yana mulki a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yehowaddin ta Urushalima.
2 Ya aikata abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji, amma bai rasa aikata laifi a zuciyarsa ba.
3 Da ya ga mulkin ya kahu a hannunsa sosai, sai ya karkashe fādawa waɗanda suka kashe tsohonsa, sarki Yowash.
4 Amma bai karkashe 'ya'yansu ba, bisa ga abin da yake a rubuce a Shari'a, wato Attaura ta Musa, inda Ubangiji ya yi umarni cewa, “Ba za a kashe iyaye saboda 'ya'yansu ba, ba za a kuma kashe 'ya'ya saboda iyaye ba, amma mutum zai mutu saboda laifin kansa.”