1 Amaziya yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara ashirin da tara yana mulki a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yehowaddin ta Urushalima.
2 Ya aikata abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji, amma bai rasa aikata laifi a zuciyarsa ba.
3 Da ya ga mulkin ya kahu a hannunsa sosai, sai ya karkashe fādawa waɗanda suka kashe tsohonsa, sarki Yowash.
4 Amma bai karkashe 'ya'yansu ba, bisa ga abin da yake a rubuce a Shari'a, wato Attaura ta Musa, inda Ubangiji ya yi umarni cewa, “Ba za a kashe iyaye saboda 'ya'yansu ba, ba za a kuma kashe 'ya'ya saboda iyaye ba, amma mutum zai mutu saboda laifin kansa.”
5 Sa'an nan Amaziya ya tattara mazajen Yahuza, ya kasa su bisa ga gidajen kakanninsu, a ƙarƙashin shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, a dukan Yahuza da Biliyaminu. Sai ya tara 'yan shekara ashirin ko fi, ya sami mutum dubu ɗari uku (300,000) ƙarfafa, waɗanda suka isa zuwa yaƙi, wato za su iya riƙon māshi da garkuwa.