8 Amma idan ka zaci ta wannan hanya ce za ka zama da ƙarfi don yaƙi, Allah zai kā da kai a gaban maƙiyi, gama Allah yana da iko ya yi taimako, ko kuwa ya ƙi.”
9 Amaziya kuwa ya ce wa annabin Allah, “To, me za mu yi yanzu game da azurfar da muka ba sojojin Isra'ila?”Sai annabin Allah ya amsa ya ce, “Ubangiji yana da iko ya ba ka fiye da haka.”
10 Sai Amaziya ya sallami rundunar sojojin da suka zo daga Ifraimu, su koma gida. Sai suka yi fushi da Yahuza ƙwarai suka koma gida cike da hasala mai zafi.
11 Amma Amaziya ya yi ƙarfin hali ya shugabanci jama'arsa, suka tafi Kwarin Gishiri, suka karkashe mutanen Seyir dubu goma (10,000).
12 Mutanen Yahuza kuma suka kama waɗansu mutum dubu goma (10,000) da rai, suka kai su a ƙwanƙolin dutse, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa daga ƙwanƙolin dutsen, duka suka yi kaca-kaca.
13 Amma sojojin rundunar da Amaziya ya sallama, bai yarda su tafi yaƙi tare da shi ba, suka faɗa wa biranen Yahuza da yaƙi, tun daga Samariya har zuwa Bet-horon, suka kashe mutum dubu uku (3,000), a cikinsu suka kwashe ganima mai yawan gaske.
14 Da Amaziya ya komo daga kisan Edomawa, sai ya kwaso gumakan mutanen Seyir, ya ajiye su su zama gumakansa, ya yi musu sujada, ya kuma miƙa musu hadaya.