1 Ahaz yana da shekara ashirin sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha shida yana mulki a Urushalima. Amma shi bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa Dawuda ya yi ba.
2 Ya aikata irin al'amuran da sarakunan Isra'ila suka yi. Ya kuma yi gumakan Ba'al na zubi.
3 Banda haka ma ya ƙona turare a kwarin ɗan Hinnom, ya ƙone 'ya'yansa maza bisa ga ƙazantattun al'adun al'ummai, waɗanda Ubangiji ya kore su daga gaban mutanen Isra'ila.
4 Ya miƙa hadayu, ya ƙona turare a masujadai da a bisa tuddai, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa.
5 Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya bashe shi a hannun Sarkin Suriya. Suka ci shi da yaƙi suka kama mutanensa da yawa, suka kai su Dimashƙu. Aka kuma bashe shi a hannun Sarkin Isra'ila, wanda ya ci shi da yaƙi, ya kashe masa mutane masu yawa.
6 Gama Feka, ɗan Remaliya, ya kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000) cikin Yahuza a rana ɗaya, dukansu kuwa jarumawa ne, don sun bar bin Ubangiji Allah na kakanninsu.
7 Sai Zikri wani ƙaƙƙarfan mutumin Ifraimu, ya kashe Ma'aseya ɗan sarki, da Azrikam, sarkin fāda, da Elkana wanda yake daga sarki sai shi.