1 Hezekiya ya ci sarauta sa'ad da yake da shekara ashirin da biyar. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Abaija, 'yar Zakariya.
2 Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa Dawuda ya yi duka.
3 A shekara ta fari ta mulkinsa, a wata na farko, sai ya buɗe ƙofofin Haikalin Ubangiji ya gyaggyara su.
4 Sai ya shigo da firistoci da Lawiyawa, ya tara su a filin da yake wajen gabas.
5 Sai ya ce musu, “Ku ji ni, ya ku Lawiyawa. Ku tsarkake kanku yanzu, ku kuma tsarkake Haikalin Ubangiji Allah na kakanninku, ku kawar da ƙazantar da yake a Wuri Mai Tsarki.
6 Gama kakanninmu sun yi rashin aminci, sun aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnmu, sun rabu da shi sun ba da baya ga mazaunin Ubangiji.
7 Sun kuma rurrufe ƙofofin shirayi suka kashe fitilu, sun daina ƙona turare ko miƙa hadayun ƙonawa a Wuri Mai Tsarki ga Allah na Isra'ila.