9 Saboda wannan an kashe kakanninmu da takobi, 'ya'yanmu mata, da 'ya'yanmu maza da matanmu, an kai su bauta.
10 “Yanzu na yi niyya a zuciyata in yi alkawari da Ubangiji Allah na Isra'ila, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da mu.
11 'Ya'yana, kada ku yi sakaci, gama Ubangiji ne ya zaɓe ku don ku tsaya a gabansa, ku yi masa hidima, ku ƙona masa turare.”
12-14 Sa'an nan sai Lawiyawa suka tashi,na Kohatawa, Mahat ɗan Amasai, da Yowel ɗan Azariya,na Merari, Kish ɗan Abdi, da Azariya ɗan Yehallelel,na Gershonawa, Yowa ɗan Zimma, da Eden ɗan Yowa,na Elizafan, Shimri da Yehiyel,na Asaf, Zakariya da Mattaniya,na Heman, Yehiyel da Shimai,na Yedutun, Shemaiya da Uzziyel.
15 Sai suka tattara 'yan'uwansu maza, suka tsarkake kansu, suka shiga bisa ga umarnin sarki, bisa ga maganar Ubangiji domin su tsabtace Haikalin Ubangiji.
16 Firistoci fa, suka shiga can cikin Haikalin Ubangiji domin su tsabtace shi. Suka kwaso dukan ƙazantar da yake a Haikalin Ubangiji, suka zuba ta a farfajiyar Haikalin Ubangiji. Sai Lawiyawa suka kwashe, suka zubar a rafin Kidron.
17 A rana ta fari a watan ɗaya suka fara aikin tsarkakewar. A rana ta takwas ga watan suka kai shirayin Ubangiji da aikin, kwana takwas suka ɗauka domin tsabtace Haikalin Ubangiji, a ranar sha shida ga watan ɗaya suka gama.