12 Guda kerub ɗin kuma, fiffikensa guda ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken shi ma ya taɓo fiffiken kerub na farko.
13 Tsawon fikafikan kerubobin ya kai kamu ashirin. Su kerubobin a tsaye suke, suna fuskantar babban ɗakin.
14 Sai ya yi labule mai launin shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau, sa'an nan ya zana siffofin kerubobin a jikin labulen.
15 Ya kuma yi ginshiƙai biyu domin ƙofar Haikalin, tsayinsu kamu talatin da biyar ne, ya yi wa ginshiƙan dajiya, tsayin kowace dajiya kamu biyar ne.
16 Ya yi sarƙoƙi, ya rataya wa ginshiƙan, ya kuma yi siffofin rumman guda ɗari, ya maƙala wa sarƙoƙin.
17 Sai ya kafa ginshiƙin a ƙofar Haikali, ɗaya a wajen kudu, ɗaya kuma a wajen arewa. Ya sa wa na wajen kudu suna Yakin, na wajen arewa kuwa Bo'aza.