19 wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko bai yi bisa kan dokar tsarkakewa na Wuri Mai Tsarki ba.”
20 Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya, ya warkar da jama'ar.
21 Jama'ar Isra'ila waɗanda suke a Urushalima kuwa sun yi idin abinci marar yisti da murna mai yawa, har kwana bakwai. Lawiyawa kuma da firistoci suka yabi Ubangiji kowace rana, suna raira waƙa da iyakar ƙarfinsu ga Ubangiji.
22 Hezekiya kuwa ya yi magana ta ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna fasaha a hidimar Ubangiji.Mutane fa suka ci abincin idin har kwana bakwai, suna miƙa hadayu na salama, suna ta yin godiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
23 Sai dukan taron suka yarda su ci gaba da yin idin har waɗansu kwana bakwai ɗin kuma, sai suka ci gaba da yin idin har kwana bakwai da murna.
24 Gama Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu bakwai (7,000), don yin hadayu, sarakuna kuma sun ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu goma (10,000). Firistoci da yawa suka tsarkake kansu.
25 Dukan taron Yahuza, da firistoci, da Lawiyawa, da dukan taron jama'a da suka zo daga Isra'ila, da baƙi waɗanda suka zo daga ƙasar Isra'ila, da baƙin da suka zauna a Yahuza, suka yi murna.