7 A wata na uku ne suka fara tattara tsibi tsibin, suka gama a wata na bakwai.
8 Sa'ad da Hezekiya da sarakuna suka zo suka ga tsibi tsibin, sai suka yabi Ubangiji da jama'arsa Isra'ila.
9 Hezekiya kuma ya yi wa firistoci da Lawiyawa tambaya a kan tsibi tsibin.
10 Sai Azariya, babban firist na gidan Zadok, ya amsa masa, ya ce, “Tun lokacin da suka fara kawo sadakarsu a Haikalin Ubangiji, mun ci mun ƙoshi, abin da ya ragu kuwa yana da yawa, gama Ubangiji ya sa wa jama'arsa albarka, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.”
11 Sai Hezekiya ya umarce su su shirya ɗakuna a Haikalin Ubangiji, suka kuwa shirya.
12 Da aminci suka kawo sadakokinsu, ta zaka da ta keɓaɓɓun abubuwa. Babban shugaban da yake lura da su kuwa, shi ne Konaniya, Balawe, da Shimai ɗan'uwansa, shi ne na biyu,
13 sa'an nan da Yehiyel, da Azaziya, da Nahat, da Asahel, da Yerimot, da Yozabad, da Eliyel, da Ismakiya, da Mahat, da Benaiya su ne shugabanni, mataimakan Konaniya da Shimai waɗanda sarki Hezekiya da Azariya babban shugaban Haikalin Allah suka naɗa.