12 Amma sa'ad da yake wahala, sai ya roƙi jinƙan Ubangiji Allahnsa, ya ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.
13 Sa'ad da ya yi addu'a gare shi, Allah ya karɓi roƙonsa da hurwarsa, ya sāke komar da shi Urushalima da mulkinsa. Sa'an nan ne Manassa ya sani Ubangiji shi ne Allah.
14 Bayan haka sai ya gina garu a bayan garin Dawuda a yammacin Gihon, a kwari har zuwa Ƙofar Kifi, ya kewaye da shi zuwa Ofel, ya gina shi da tsayi sosai. Sa'an nan ya sa sarakunan yaƙi a garuruwa masu garu na Yahuza.
15 Ya kwashe gumaka da siffofi daga cikin Haikalin Ubangiji, da dukan bagadan da ya giggina a bisa dutse na Haikalin Ubangiji da a Urushalima. Ya zubar da su a bayan birnin.
16 Ya kuma komar da bagaden Ubangiji, ya miƙa hadayu na salama da na godiya, ya kuma umarci Yahuza ta bauta wa Ubangiji Allah na Isra'ila.
17 Duk da haka dai jama'a suka ci gaba da miƙa hadayunsu a masujadai, amma ga Ubangiji Allahnsu kaɗai.
18 Sauran ayyukan Manassa, da addu'o'insa zuwa ga Allahnsa, da abubuwan da masugani suka faɗa sa'ad da suka yi masa magana da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila, suna cikin littafin tarihin sarakunan Isra'ila.