19 Addu'arsa, da yadda Allah ya karɓi roƙonsa, da dukan zunubinsa, da rashin amincinsa, da wuraren da ya gina masujadai, ya kafa Ashtarot da siffofi, kafin ya ƙasƙantar da kansa, suna nan a rubuce a littafin Hozai.
20 Haka fa Manassa ya rasu, suka binne shi a gidansa, sai Amon ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.
21 Amon yana da shekara ashirin da biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara biyu yana mulki a Urushalima.
22 Shi ma ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Manassa, tsohonsa, ya yi. Amon ya miƙa hadaya ga dukan siffofin da tsohonsa, Manassa, ya yi ya bauta musu.
23 Bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji yadda tsohonsa, Manassa, ya yi ba, amma shi Amon ya yi ta yin zunubi a kai a kai.
24 Sai fadawansa suka yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidansa.
25 Jama'ar ƙasar kuwa suka karkashe dukan waɗanda suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiyar, suka naɗa Yosiya, ɗansa, ya gāji gadon sarautarsa.