1 Sulemanu ya kammala dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sa'an nan ya kawo kayayyakin da tsohonsa Dawuda ya riga ya keɓe, wato azurfa da zinariya, da dukan kayan girke-girke, da tasoshi, ya ajiye su a taskokin Haikalin Allah.
2 Sulemanu kuwa ya tattara dattawan Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin gidajen kakannin jama'ar Isra'ila, a Urushalima, domin a yi bikin fito da akwatin alkawari na Ubangiji da yake a alfarwa a birnin Dawuda, wato Sihiyona.
3 Sai dukan mutanen Isra'ila suka hallara a gaban sarki, a wurin bikin, a wata na bakwai ke nan.
4 Sa'an nan dukan dattawan Isra'ila suka zo, Lawiyawa kuwa suka ɗauko akwatin.
5 Suka kuma kawo akwatin, da alfarwa ta taruwa, da dukan tsarkakakkun kayayyakin da suke cikin alfarwar. Lawiyawa da firistoci ne suka kawo su.
6 Sarki Sulemanu da dukan taron mutanen Isra'ila waɗanda suka hallara a gaban akwatin suka yi ta miƙa hadayun tumaki da bijimai masu yawan gaske, har ba su ƙidayuwa.