13 Sulemanu ya riga ya yi dakali na tagulla, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, tsayinsa kamu uku, ya ajiye shi a tsakiyar filin, ya tsaya a kai. Ya durƙusa a gwiwoyinsa, a idon dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ɗaga hannuwansa sama,
14 ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ba wani Allah kamarka a sama ko a duniya, wanda yake cika alkawari, kana nuna madawwamiyar ƙauna ga bayinka masu tafiya a gabanka da zuciya ɗaya.
15 Kai ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka, tsohona Dawuda. Abin da ka faɗa ka kuma aikata.
16 Yanzu fa, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka tsohona cewa, ‘Daɗai, ba za a rasa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai 'ya'yanka maza za su lura da al'amuransu, don su yi tafiya bisa ga shari'ata, yadda kai ka yi tafiya a gabana.’
17 Saboda haka, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka Dawuda.
18 “Ashe kuwa Allah zai zauna tare da ɗan adam a duniya? Ga shi kuwa, sama da saman sammai ba su iya ɗaukarka ba, balle fa ɗakin da na gina.
19 Duk da haka ka kula da addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa. Ya Ubangiji Allahna, ka kasa kunne ga kuka da addu'ar da bawanka yake yi a gabanka.