15 Kai ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka, tsohona Dawuda. Abin da ka faɗa ka kuma aikata.
16 Yanzu fa, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka tsohona cewa, ‘Daɗai, ba za a rasa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai 'ya'yanka maza za su lura da al'amuransu, don su yi tafiya bisa ga shari'ata, yadda kai ka yi tafiya a gabana.’
17 Saboda haka, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka Dawuda.
18 “Ashe kuwa Allah zai zauna tare da ɗan adam a duniya? Ga shi kuwa, sama da saman sammai ba su iya ɗaukarka ba, balle fa ɗakin da na gina.
19 Duk da haka ka kula da addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa. Ya Ubangiji Allahna, ka kasa kunne ga kuka da addu'ar da bawanka yake yi a gabanka.
20 Ka dubi wajen Haikalin nan dare da rana, wurin da ka yi alkawari za ka sa sunanka, ka kasa kunne ga addu'ar da bawanka zai yi wajen wannan wuri,
21 ka ji roƙe-roƙen bawanka da na jama'ar Isra'ila, sa'ad da suke addu'a suna fuskantar wannan wuri, ka ji daga wurin da kake zaune a Sama, sa'ad da ka ji, ka gafarta.