6 Amma na zaɓi Urushalima domin sunana ya kasance a wurin, na kuma zaɓi Dawuda ya zama shugaban jama'ata Isra'ila.’
7 “Ya zama kuwa tsohona Dawuda ya yi niyyar gina Haikali domin sunan Ubangiji, Allah na Isra'ila.
8 Amma Ubangiji ya ce wa ubana Dawuda, ya kyauta, tun da yake ya yi niyya a zuciyarsa zai gina ɗaki saboda sunansa.
9 Duk da haka, ba shi zai gina Haikalin ba, ɗansa wanda za a haifa masa, shi ne zai gina Haikalin domin sunansa.
10 “Yanzu fa Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na gāji matsayin ubana Dawuda, na kuwa hau gadon sarautar Isra'ila, yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuwa gina Haikali domin sunan Ubangiji, Allah na Isra'ila.
11 A can na ajiye akwati inda aka sa alkawarin da Ubangiji ya yi wa jama'ar Isra'ila.”
12 Sulemanu ya miƙe a gaban bagaden Ubangiji a idon dukan taron Isra'ila ya ɗaga hannuwansa.