1 Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.
2 Amos ya ce,“Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona,Muryarsa za ta yi tsawa dagaUrushalima.Da jin wannan, sai wuraren kiwo zasu bushe,Ƙwanƙolin Dutsen Karmel, da yakekore zai yi yaushi.”
3 Ubangiji ya ce,“Mutanen Dimashƙu sun ci gaba dayin zunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun zalunci mutanen Gileyad dazalunci mai tsanani.
4 Don haka zan aukar da wuta a kanfādar Sarkin Suriya.Za ta ƙone kagarar Ben-hadad,sarki.
5 Zan ragargaje ƙyamaren ƙofofinbirnin Dimashƙu,In kawar da masu sarautar Bet-edenda na kwarin Awen.Za a kwashe mutanen Suriya ganimazuwa ƙasar Kir.”
6 Ubangiji ya ce,“Mutanen Gaza sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun kwashe al'umma duka, sunsayar wa mutanen Edom.