5 Zai yiwu tsuntsu ya fāɗi ƙasaIn ba a kafa masa tarko ba?Zai yiwu tarko ya zarguIn bai kama wani abu ne ba?
6 Zai yiwu mutane su rasa firgita,Idan aka busa ƙahon yaƙi abirni?Zai yiwu wata babbar masifa ta aukowa birniBa da yardar Ubangiji ba?
7 Hakika Ubangiji ba yakan aikatakome ba,Sai da sanin bayinsa annabawa.
8 Zaki ya yi ruri!Wa ba zai ji tsoro ba?Sa'ad da Ubangiji ya yi magana!Wa zai ƙi yin shelar maganarsa?
9 Ka yi shela ga mazaunan fādar Ashdod da Masar, ka ce, “Duk ku taru a Samariya ku ga irin babban shashancin da ake yi a can, ku ga irin laifofin da ake aikatawa a birnin.”
10 Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane suka cika gidajensu masu daraja da abubuwan da suka samo ta hanyar zamba, da ta kama-karya. Ta yadda za su yi su yi aminci ma, ba su sani ba.
11 “Saboda haka abokan gaba za sukewaye ƙasarsu,Su hallakar da kagaransu,Su washe gidajen nan nasu masudaraja.”