19 Zai zama kamar wanda ya tsere wazakiYa fāɗa a bakin beyar!Ko kuwa kamar wanda ya komogida,Ya dāfa bango, maciji ya sare shi.
20 Ranar Ubangiji za ta kawo baƙinciki,Ba murna ba.Rana ce ta damuwa ba ta fara'a ba.
21 Ubangiji ya ce,“Na ƙi bukukuwanku na addini.Ina ƙyamarsu!
22 Sa'ad da kuka kawo mini hadayunƙonawaDa hadayunku na tsaba, ba zankarɓa ba.Ba kuma zan karɓi turkakkundabbobinkuWaɗanda kuka miƙa mini hadayungodiya ba.
23 Ku yi shiru da yawan hargowarwaƙoƙinku.Ba na so in saurari kaɗe-kaɗenku dabushe-bushenku.
24 Sai ku sa adalci da nagarta su gudanoa yalwaceKamar kogin da ba ya ƙafewa.
25 “Ya ku, jama'ar Isra'ila, ai, a waɗannan shekaru arba'in da kuka yi cikin jeji kuka kawo mini sadaka da hadayu,